’Yan bindiga sun hallaka dan takarar shugaban kasa a wurin taron yakin neman zabensa, kwana 10 kafin zaben shugaban kasa a kasar Ecuador.
A ranar Laraba jaridar El Universo ta kasar ta ruwaito cewa Villavicencio ya rasu bayan mahara sun yi masa harbi uku a kansa a lokacin da ake tsaka da gudanar da yakin neman zabe a Quito, babban birnin kasar.
- Tsohon madugun ’yan tawaye ya kafa kungiyar neman mai da Bazoum kan mulkin Nijar
- Abin da Sanusi II ya tattauna da gwamnatin sojin Nijar
Rahoton ya ce wasu mutum takwas sun jikkata a harin, inda aka garzaya da bakwai daga cikinsu asibiti daga wurin taron.
Shugaban kasar mai barin gado, Guillermo Lasso, ya tabbatar da rasuwar Fernando Villavicencio, yana mai cewa gwamnati ba za ta bari jininsa ya tafi haka nan ba.
“Na kadu da kisan da aka yi wa dan takarar shugaban kasa Fernando Villavicencio,” in ji shi a cikin sakon ta’aziyyar da ya wallafa a Twitter.
Ya kara da cewa bisa la’akari da gudunmawar mamacin da kuma irin fafutukarsa a ksar, gwamnati za ta tabbatar an hukunta wadanda suka kashe shi.
Daga bisani gwamnatin kasar mai barin gado ta ayyana dokar ta-baci na tsawon wata shida a fadin kasar.
Villavicencio mai shekaru 59 sanannen mutum ne wajen adawa da rashawa da kuma manyan laifuka a kasar Ecuador.
A ranar 20 ga watan nan na Agusta za a gudanar da zaben shugaban kasar, ko da yake rahotanni sun nuna Villavicencio ba shi da yawan magoya baya da zai iya lashe zaben.