Mahara sun bindige wani hafsan dan sanda sannan suka yi garkuwa da mutane a unguwar Babbar Saura da ke garin Kaduna.
Kusan mako guda ke nan da ake fama da hare-haren ’yan bindiga masu garkuwa da mutane a Jihar Kaduna.
- Rufe iyakoki bai hana fasakwaurin makamai ba —Buhari
- Majalisar Malamai ta nemi Ganduje ya cire wa Abduljabbar takunkumi
- Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan wata shida a Dubai
- Ba sace ni aka yi ba, guduwa na yi – Amaryar Kano
Majiyarmu ta ce maharan sun kai harin ne a ranar Laraba da dare inda suka bindige dan sandan mai mukamin Sufeto a gidansa, sannan suka yi awon gaba da wasu mutane, ciki har da wani dan banga.
Wani jami’in tsaron sa kai a Babbar Saura da ya nemi kar a bayyana sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, “Gaskiya ne [masu garkuwa da mutane] sun shigo unguwarmu amma mun yi musayar wuta da su kuma a lokacin ne biyu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su suka samu tserewa, amma sun tafi da wata budurwa da wani dan banga bayan sun kashe wani dan sanda mai mukamin Sufeto.’’
Jami’in ya yaba da yadda jami’an tsaro suka yi saurin kawo agaji bayan an sanar da su ta waya game da harin.
Aminiya ta yi kokarin samun karin bayani daga mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, amma ya ce daga baya zai yi bayani.
Wakilinmu ya kara kiran shi amma bai dauki wayar ba.