✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe dan sanda a harin ISWAP a Borno

An yi artabu tsakanin bangarorin biyu.

Wani dan sanda daya ya rasa ransa yayin harin da mayakan ISWAP suka  kai a yankin  Magumeri da ke Jihar Borno.

A rahoton da aka tattaro ya nuna cewa maharan sun yi wa jami’an ’yan sanda dirar mikiya da misalin karfe 2 na rana a kan wata motar Hilux daya da babura.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan sun yi wa ’yan sandan kwanta-kwanta ne bayan sun ajiye motarsu, sannan suka  yi sandar shiga wurin da kafa don gujewa duk wani yunkuri da zai kawo musu tirjiya.

Wata majiyar ’yan sanda, ta shaida wa Zagazola Makama, Kwararre kan Yaki da Tayar da Kayar Baya kuma Mai Sharhi kan Harkokin Tsaro a Gabar Tafkin Chadi cewa, ’yan ta’addar sun kai hari kan  ’yan sandan ne ta bangarori biyu daban-daban wanda ya yi sanadin mutuwar wani dan sanda guda mai mukamin sajen

Majiyar ta kara bayyana cewa, sai dai ’yan sandan sun mayar da martani cikin gaggawa inda aka shafe kusan mintuna 30 ana artabu a tsakanin bangarorin biyu, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa.

Sai Makama ya ce ’yan ta’addan sun samun nasarar tserewa da wata motar ’yan sanda guda daya ta rundunar Crack Operative.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Borno, Abdu Umar, ya tabbatar da faruwar wannan hari da mayakan na ISWAP masu da’awar jihadi a Yammacin Afirka suka kai.