Wasu da ba a sani ba sun kashe wani basarake suka kuma kona mutum uku a cikin ’yan tawagarsa da ransu a yankin Alagodo da ke Karamar Hukumar Ewekkoro ta Jihar Ogun.
Majiyar Aminiya ta ce wasu ’yan daba ne suka tare Oba Ayinde Odetola ne tare da abokansa suna dawowa daga rangadi, suka kashe shi sannan suka kona abokan nasa da ransu, bayan barkewar rikicin sarautar Alagodo da ke Kasar Egba.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Gwamnatin Kano Na Dakatar Da Makarantu Masu Zaman Kansu
- A shirye nake in sa hannu a hukuncin kisa kan makashin Hanifa – Ganduje
Majiyar ta ce tun bayan kisan da aka yi wa basaraken da abokan nasa da misalin karfe 11 na ranar Litinin, wasu mazauna yankin suka fara kaura daga garin.
Rikicin ya kunno kai ne bayan takaddama a kan wanda za a ba wa sauratar yankin a tsakanin ’yan kabilar Ake da kuma kabilar Owu da ke zaune a yankin na Kasar Egba.
Oba Ayinde Odetola da aka kashe dai dan kabilar Ake ne a Kasar Egba, inda wadansu mazauna suke bore a kan cewa babu yadda za a ayi dan kabilarsa ya mulki masarautar saboda ’yan kabilar Owu ne ke da rinjayen al’umma.
Majiyoyi a yankin Kasar Egba sun tabbatar mana cewa ko a kwanakin baya sai da aka yi wa wani kasin Oba Otedola kisan gilla a sakamakon rikicin.
Wata ’yar uwar Oba Odetola mai suna Cif Adenike Akintade, ta ce, “Yau (Litinin) da safe na aka sallamo ni daga asibiti, ga shi kuma na shiga halin juyayin rasuwar dan uwana da aka kashe da misalin karfe 11 na safe.
“Ranar Asabar Mai Martaba ya kira ni, cewa in rage wasu abubuwan da nake yi saboda gajiya na ira kara min rashin lafiyata.
“A watannin baya Oba Odetola ya rasa kaninsa a rikicin; ’yan daba ne suka kashe shi, ga shi yau kuma Mai Martaba ya bar duniya.”
A ranar Litinin da dare ne dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa maharan sun kona motar basaraken bayan sun kashe shi.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole tare da Mashawarcin Gwamna Dapo Abiodun, wato Olusola Subair, sun ziyarci garin domin gane wa kansu abin da ya faru.
A cewarsa, duk da cewa babu wanda aka kama a kan zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya umarci sashen ’yan sanda masu binciken laifukan kisa da ya gudanar da bincike a kan al’amarin.