✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe 109 an jikkata 655 a hatsari cikin wata takwas

Akalla mutum 109 ne suka mutu baya ga wasu 655 da suka samu raunuka sakamakon hatsari a watanni takwas da suka gabata a Jihar Ogun.…

Akalla mutum 109 ne suka mutu baya ga wasu 655 da suka samu raunuka sakamakon hatsari a watanni takwas da suka gabata a Jihar Ogun.

Hukumar Kula da Bin Dokokikin Hanya ta Jihar (TRACE) ta ce asarar da aka tafka a hadurra guda 527 ta auku ne sakamakon tukin ganganci da gudun da ya wuce ka’ida da fashewar taya rashin sa damar tuki da dangoginsu.

Kakakin Hukumar, Babatunde Akinbiyi, ya sanar a ranar Asabar cewa 83 daga cikin rayukan da aka rasa maza ne sai kuma mata 26.

Akinbiyi ya ce hadduran mota sun yi ajalin mutum 74, yayin da wasu 35 suka rasu a na babura daga watan Janairu zuwa Agustan 2020.

Ya kuma ce 487 daga cikin wadanda suka samu raunuka mazan ne da mata 178.

Jami’in ya jaddada kira ga masu ababen hawa da su kiyaye ka’idojin tuki da wuraren da aka hade hanyoyi, yana mai jaddada aniyar hukumarsa ta tabbatar da kariya da kuma wayar da kan masu amfani da hanya.