✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama ‘yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin N8.5m

An sallami wasu ’yan sanda uku daga bakin aiki saboda karɓar na-goro da saba wa ƙa’idar aiki a Bayelsa.

An karrama wasu jami’an ‘yan sanda hudu da lambar yabo a Jihar Taraba saboda ƙin karɓar cin hancin Naira miliyan 8.5 a hannun wani wanda ake zargi da ta’adar garkuwa da mutane.

Kwamishinan ’yan sanda, CP David Iloy Anomon ne ya miƙa wa ’yan sandan lambobin yabon yayin bikin karramawar da aka gudanar wannan Juma’ar a ofishinsa da ke Jalingo.

Ya yaba wa ’yan sandan kan irin wannan hali nagari na riƙon amana da kishin ƙasa da suka nuna a yayin gudanar da ayyukansu.

“Ya zama wajibi mu karrama waɗannan jami’ai da suka haɗiye duk wani kwaɗayi yayin da suka kafa shingen binciken ababen hawa a kan hanyar Jalingo zuwa Yola.

“Duk da yawan kuɗin da waɗanda ake zargi suka bai wa jami’an a matsayin cin hanci, sun nuna jarumta ta ƙin karɓa sannan suka kama su,” a cewar CP Iloy.

Aminiya ta ruwaito cewa, jami’an ’yan sandan da aka karrama sun haɗa da Insfeta Difference Tih da Insfeta Ngamarju Gambi da Insfeta Usman Haruma da kuma Kofura Zurudeen Mamuda.

Da suke magana da manema labarai, jami’an ’yan sandan sun yi wa Kwamishinan Iloy godiya da ya wannan karamci.

Kazalika, sun ce hakan ya ƙara musu ƙaimi na ci gaba da jajircewa wajen yi wa kasarsu hidima da mayar da hankali kacokam wajen dakile masu aikata miyagun ayyuka.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan dai na zuwa ne a yayin da a can Jihar Bayelsa kuma aka sallami wasu jami’an ’yan sanda uku daga bakin aiki saboda karɓar na-goro da sauran ayyukan rashawa da suka saba wa ƙa’idar aikinsu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa, CSP Ikwo Kelvin Lafieghe ta fitar a wannan Juma’ar, ta ce an ɗauki matakin ne domin tsaftace rundunar daga bara-gurbi.

Ta bayyana cewa jami’an ’yan sandan da aka sallama sun haɗa da Insfeta Edet Inamete da Insfeta Jeremiah Oreeke da Insfeta Uche Collins.