Shugaban Kasar Zambiya, Hakainde Hichilema, ya karrama tsohon Shugaban Najeriya, Oluwasegun Obasanjo, da lambar yabon kasar mafi girma, wato ‘Order of the Eagle’.
Haka nan, tsohuwar shugabar kasar Laberiya, Ellen Johnson Sirleaf da takwaranta ta kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, su ma sun samu irin wannan karramawar da Obasanjon ya samu.
Karrama su ne a wani biki da aka gudanar ranar Alhamis a Lusaka, babban birnin kasar.
Hadimin Obasanjo kan sha’anin yada labarai, Kehinde Akinyemi, ya ce bayanin karramawar na kunshe ne cikin wata sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar a ranar Larabar da ta gabata.
Akinyemi ya ce sanarwar ta sanar da al’umma yadda Sakataren Riko na gwamnatin kasar, P.K Kangwa ya sanya hannu kan mika lambobin yabon.
Da yake jawabi a madadin wadnda aka karrama din, Obasanjo ya ce karramawar za ta kara musu kwarin gwiwa wajen hidimta wa Afirka don ci gabanta.