Shugaban jamhuriyyar Nijar mai barin gado, Mahamadou Issofou, ya karrama Shugaba Muhammadu Buhari da lambar yabo mafi girma ta kasar Nijar saboda rawar da gwamnatinsa ta taka wajen inganta huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
Wannan na zuwa yayin da Shugaba Issofou ya kai ziyarar aiki a Najeriya inda ya gana da Shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata.
- Yaro mafi kiba a duniya ya rage nauyi da kilo 107
- Mahara sun bindige mutum 55 a Nijar
- Boko Haram ta kona asibiti da makaranta a Yobe
Shugaban Issofou ya yaba wa Najeriya musamman a kan dangartakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fagen yaki da ’yan ta’adda da suka uzzura wa kasashen biyu.
Daga bisani Shugaba Issofou wanda zai sauka daga mulki a watan gobe, ya kaddamar da wata hanyar da aka sanya sunansa a Abuja, inda ya samu rakiyar Gwamnonin Jihohin Kebbi, Zamfara, Katsina, Jigawa, Sakkwato, Kano da Yobe.
A nasa jawaban, Shugaba Buhari ya yaba wa takwaran nasa dangane da salon jagorancinsa na yaki da talauci a tsakanin al’umma.
Kazalika, Buhari ya yaba wa Shugaba Issofou kan tsayuwar dakan da ya yi ta kin amincewa da sauya kundin tsarin mulkin kasar da zai bashi damar ci gaba da kasancewa a kan gado na mulki.
A baya bayan nan ne Shugaba Issofou ya lashe lambar girma ta Gidauniyar Mo Ibrahim mai dauke da kyautar Dala Miliyan biyar saboda nagartar da ya nuna yayin jagorancin kasarsa.