✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce:

525. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Isah ya ba ni labari daga As-Sauri daga Khalid dan Ma’abadan daga Mikdad (Allah Ya yarda…

525. An karbo daga Ibrahim dan Musa ya ce: “Isah ya ba ni labari daga As-Sauri daga Khalid dan Ma’abadan daga Mikdad (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (SAW) ya ce, “Babu abin da ya fi alheri ga mutum irin ya ci daga abin da ya aikata da hannunsa. Domin lallai Annabin Allah Dauda (AS) ya kasance yana ci daga abin da hannunsa ya aikata.”

526. An karbo daga Yahya dan Musa ya ce: “Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Hammam dan Munabbih ya ce, Abu Huraira daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Lallai Dauda (AS) ya kasance yana ci abinci daga abin da ya aikata da hannunsa.”

527. An karbo daga Yahaya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari, daga Ukail daga dan Shihab daga Abu Ubaid bawan Abdurrahman dan Aufu cewa: “Lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) yana cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Da dai dayanku zai tafi ya yiwo kayan (rungumen) itace bisa bayansa, shi ya fi masa alheri da ya roki wani ya ba shi ko ya hana shi.”

528. An karbo daga Yahya dan Musa ya ce: “Waki’u ya ba mu labari ya ce, Hisham dan Urwat ya ba mu labari daga Babansa daga Zubair dan Awwam (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Da dai dayanku ya dauki igiyarsa, zuwa samo itace ya sayar ya fi masa daga roko.”

Babi na Goma Sha Bakwai: Sauki da rangwame a cikin saye da sayarwa. Wanda yake neman wani hakki to ya neme shi da tausasawa:

529. An karbo daga Aliyu dan Ayyash ya ce: “Abu Ghassan ya ba mu labari ya ce, Muhammad dan Munkadir ya ba ni labari daga Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce, “Allah Ya jikan mutumin da ke da rangwame idan zai sayar kuma haka idan zai saya. Da kuma lokacin neman biyan bashi (karban kudin bashi).”

Babi na Goma Sha Takwas: Wanda ya saurara wa mara shi game da biyan bashi:

530. An karbo Ahmad dan Yunus ya ce: “Zuhair ya ba mu labari ya ce, Mansur ya ba mu labari cewa, lallai Rabi’ata dan Hirash ya ba shi labari cewa: Lallai Huzaifa (Allah Ya yarda da shi) ya ba shi labari ya ce, “Annabi (SAW) ya ce, “Mala’iku sun taba karban ran wani mutum da ke gabaninku sai suka ce, “Shin ka san wani aikin alheri da ka taba aikatawa? Ya ce, “Na kasance ina umartan yarana da su rika saurara wa mai bashi, kuma ina umartarsu da yafe wa mai tsananin talauci. (Annabi) ya ce, “Sai aka yafe masa laifuffukansa.” Abu Abdullahi ya ce, “Abu Malik ya ce, daga Rabi’u ya ce, “Na kasance ina saukakawa ga mara shi, kuma ina saurara wa mai tsanani…..”

Babi na Goma Sha Tara:Wanda ya saurara wa mai tsanani:

531. An karbo daga Hisham dan Ammar ya ce: “Yahya dan Hamza ya ba mu labari, ya ce, “Zubaidi ya ba mu labari daga Zuhuri daga Ubaidullahi dan Abdullahi cewa: Lallai shi ya ji Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce, “An taba wani mai arziki (dukiya) yana ba mutane bashi, idan ya ga mai tsanani sai ya ce, wa samarukansa (yaransa) ku yafe masa mai yiwuwa Allah Ya yafe mana. Sai Allah Ya yafe masa.”