Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da karin wa’adin shekarun yin ritaya ga malaman makarantun Firamare da na Sakadire da ma na Manyan Makarantu mallakin jihar zuwa 65.
Ya sanar da hakan ne yayin bikin bayar da kyaututtuka da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen jihar Kano ta shirya domin bikin Ranar Ma’aikata da ya gudana ranar Asabar.
Kazalika, Ganduje ya amince da shekaru 40 a matsayin shekarun da malaman za su iya shafewa suna aiki a jihar.
Gwamnan ya ce, “Tun da jimawa, Gwamnatin Tarayya ta amince da makamancin wannan tsarin, saboda haka muma muka ga bai kamata a bar ma’aikatan Kano a baya ba.
“Saboda haka daga yanzu, malamanmu da lakcarorinmu suma za su fara cin gajiyar wannan karin shekarun zuwa 65, yayin da shekarun aiki kuma muka kara su daga 35 zuwa 40.
“Mun kirkiro manufofi da dama da za su inganta harkar koyo da koyarwa a jihar Kano, ciki har da tsarin taimakekkniyar lafiya ga malaman da iyalansu, wanda tsarinmu a yau yana daya daga cikin mafiya inganci a Najeriya,” inji Gwamnan.
Ganduje ya kuma ce a irin hobbasan da Gwamnatinsa take yi na bunkasa ilimin, ta kirkiro tsarin bayar da ilimi kyauta kuma dole ga dukkan yaran dake jihar.
Yayin bikin dai, Gwamnan ya kuma gabatar takardar daukar aiki ga wata budurwa malamar asibiti da ta sahfe shekaru 15 tana aiki a matsayin ma’aikaciyar wucin gadi a Asibitin Hotoro wacce ta rasa kafafunta a bakin aiki.
Tun da farko a jawabinsa, Shugaban NLC na Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya ce sun shirya taron ba da kyaututtukan ne da nufin karrama wadanda suka zama zakarun gwajin dafi wajen kiyaye dokokin aiki a jihar.