An kara sako hudu daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin da aka kai wa jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.
Tukur Mamu, mawallafin da ke zaune a Kaduna, wanda ya shiga tsakani a sakin wasu fasinjojin ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a Juma’ar nan.
- Gwamnati ta rufe kamfanonin Takin Zamani 4 a Kano
- LABARAN AMINIYA: Ya Kamata Dalibai Su Maka ASUU A Kotu —Ministan Ilimi
Daga cikin wadanda suka kubuta kamar yadda Mamu ya tabbatar har da wata dattijuwa mai shekara 90, Halimatu Atta da wata ’yarta mai shekara 53, Adama Atta Aliyu.
“Ina mai ba da tabbacin cewa, an sako karin mutum hudu daga cikin fasinjojin jirgin kasan wadanda babu jimawa suka bar ofishina.
“Cikin wadanda suka kubuta, har da wata tsohuwa mai shekara 90, Mama Halimatu da ’yarta mai shekara 53, Adama Aliyu Atta, wadda ita ce matar da ta yi jarumtar kalubalantar azabtarwar da ’yan bindigar suka rika yi musu a wani bidiyo da suka saki a kwanan baya.
“Sun kawo min ziyara ne baki dayansu domin mika godiyarsu kan rawar da na taka a baya ta shiga tsakani wajen ganin an saki fasinjojin da aka yi garkuwa da su.
“Sun kuma bukaci gwamnati ta ci gaba da kokari don ganin sauran fasinjojin 23 da suka rage a hannun ’yan bindigar a daji sun kubuta, don a cewarsu sun baro su cikin hali na ban tausayi.”
Aminiya ta ruwaito cewa, sauran wadanda suka kubutar sun da wani Mohammed Sani Abdulmajid (M. S Ustaz) da kuma wani dan asalin Jihar Sakkwato, Alhaji Modin Modi Bodinga.