Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta kame wata mata mai shekara 20, Miracle Kalu, bisa zargin ta sayar da jaririyarta ’yar wata guda da haihuwa kan kudi N130,000.
Kame matar ya biyo bayan kame wasu mutum hudu, ciki har da wasu ma’aurata, bisa zargin sun yi yunkurin sake sayar da jaririyar a Legas da kuma wasu ma’auratan bisa zargin fansar jaririyar.
Ma’uaratan da suka yi yunkurin sayar da jaririyar su ne Patrick Mbama da Ogechi Chinonso Ekwebele; an yi zargin sun sayi jaririyar daga matar a jihar Imo inda suka sayar ga wasu ma’auratan a Legas kan kudi N150,000.
- An kama matar da ta saci jaririn wata 4 a Ogun
- Kotu ta daure matar aure shekara 3 saboda satar jariri
Binciken da aka yi
’Yan sanda sun ce bincikensu ya nuna cewa mutanen biyu Mbama da Ekwebele ba su taba auren juna ba amma sun yi karyar cewa su ma’aurata ne domin kawai su samu damar yin fataucin jaririyar zuwa birnin Legas.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedkwatar rundunar ’yan sandan da ke Ikeja, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya ce ’yan sanda sun jiyo kukan jaririyar a cikin wata mota kirar Toyota Sienna sannan sai suka shawarci Madam Ekwebele, wacce ita ce ya kamata ta zama uwar jaririyar, domin ta ba ta mama, amma sai ta nuna dardar da aikata hakan, lamarin da ya haifar da dora karan zargi a kanta.
Yadda aka kama wadanda ake zargi
Kwamishinan ’yan sandan ya ce, “A ranar 26 ga watan Afrilu da misalin karfe 2 na dare, ’yan sandan jihar yayin sintiri sun kame wata mota kirar Toyota Sienna SUV dauke da fasinjoji bakwai.
“A cikin fasinjojin akwai wasu masu suna Patrick Mbama da Ogechi Chinonso Ekwebele, suna cikin tafiya tare da wata jaririya ’yar kimanin wata guda a duniya, ana zargin sato ta aka yi.
“Sun taho ne daga garin Orlu, a jihar Imo. Dukkan wadanda suke cikin motar an kame su kan karya dokar nan ta hana zirga-zirga tsakanin jihohin kasar nan; kuma an rike motar.
“Da aka dakatar da su, sai wadannan ma’auratan suka ce wai ai wasu mutum biyu mace da namiji ne da ba su da da suka sayi jaririn.
“Ma’uaratan biyu da ba su da dan, Izuchukwu Okafor, mai shekara 51 da Cecilia Okafor mai shekara 40, da suka ba da umarnin sayan jarirriyar, suma sun shiga hannu.”
Abin da wacce ake zargin ta ce
Matar ta gaya wa manema labarai cewa ita marainiya ce kuma ta ajiye karatun sakandare.
Ta kuma ce, “Lokacin da na samu juna biyu saurayina, wanda ban san gidansa ba, ya ki yarda da cikin, yana mai cewa ba shi ne ya yi mini shi ba.
“Ganin ina zaune tare da ’yar uwata wacce ita ma take fama da halin yau, lallai ne na fita daga gidan domin samar wa kaina mafitar rayuwa.
Abin da yasa na sayar da jaririyar
“Na haife ta ne a asibitin karbar haihuwa na God’s Own Maternity da ke jihar Imo kuma na sayar da ita ne domin na samu damar kulawa da gyambon cikin da ke damu na.
“Dalilin ke nan da kuma matsalar rashin kudi ta sa na sayar da jaririyata ’yar kwanaki 28 ga matar mai suna Cecilia Okafor. Na sayi magunguna domin kula da lafiyar jikina da kudin da na sayar da jaririyar.”
Rashin haihuwa
Cecelia Okafor ta ce zakuwarta ta samun “da nata” ya sanya ta fada harkar sayan wannan jaririyar.
“Rashin samun haihuwa na tsawon shekara 15 ba abu ne mai sauki ba. Na ji labarin akwai wata da take da juna biyu kuma bata son jaririyar.
“Sai na yi ta daukar dawainiyarta tun kafin ta haihu har sai bayan haihuwar. Ta gaya mini cewa ita marainiya ce kuma tana da cutar numfashi ta asthma hakan ne dalilin da ya sa ta yarda ta sayar da jaririyar.
“Na sayi jaririyar kan N130,000,” inji ta.