An tsare wasu ’yan sanda biyar da aka kama suna rakiya da ba da kariya ga dillalan miyagun kwayoyi wajen yin safarar hodar Iblis.
Dubun ’yan sandan da ake tsare a halin yanzu ta cika ne a lokacin da suke rakiyar dilar hodar Iblis mai tarin awa da misalin karfe 3 na asuba a Jihar Legas.
Wadanda aka kama din suna aiki ne a runduna ta musamman na shugaban ’yan sanda kan yaki da muggan laifuka.
An kama su ne bayan musayar wuta da ’yan sandan farin kaya da suka samu labarin mugun aikin, suka kuma yi kokarin kama dillalan kwayoyin a yankin Vicoria Island.
- Abin da malamai suka tattauna da Babban Hafsan Tsaro kan Harin Kaduna
- EFCC ta kama tagwaye ’yan yahoo
Wani babban dan sanda ya shaida wa wakilinmu cewa bayan an tsayar da wadanda ake zargin domin bincike sai “suka fara barazana ga jami’anmu suna harbi a iska.
“Amma duk da haka, jami’anmu suka ki janyewa su bar su su wuce, da aka bincika kuma sai aka kama su da tulin miyagun kwayoyi,” wadana bayanai suka nuna hodar iblis ce.
Jami’in ya ci gaba da cewa, “ana cikin haka sai jami’an NDLEA suka iso wurin, amma da suka nemi su tafi da kwayoyin sai wadancan suka ci gaba da harbe-harbe, suna neman hana su.
“Hakan ne ya sa sojoji suka iso wurin, suka tafi kwayoyin barikinsu da ke Bonny Camp, daga nan kwamandansu ya kira AIG mai kula da Zone 2, aka zo aka tafi da ita.”
Wadanda aka kaman sun a cewarsa, sun hada da wani mukamin DSP, Fayomi Abraham, ASP Emmanuel Bentong, Inspector Salami Femi, Inspector Ashimi Adedokun da Sajan Alex Akeredolu.
Wani mai mukamin mataimakin Kwamishinan ’yan sanda Ali Mohammed Ari ne ya kai su ofishin AIG Ali domin fuskanar bincike in ji jami’in.
Wakilinmu ya nemi AIG mai kula da Zone 2, Ali Mohammed Ari, domin karin amma bai amsa kiran ba.