✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yan ina-da-kisa 47 a Kwalejin Tarayya a Kebbi

Sun sari jami’in tsaron kwalejin da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama.

’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar makarantar suka kutsa cikinta da garken shanu sama da 300.

Ya ce da shigarsu ke da wuya. sai suka zarce zuwa ɓangaren gidajen ma’aikata suka lalata musu haki.

Ya ƙara da cewa makiyayan sun kuma sari wani jami’in tsaron makarantar da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama.

“A sakamakon haka ya samu karaya a ƙafar damsa kuma yanzu ana jinyar sa a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Birnin Kebbi,” in ji CSP Nafi’u Abubakar.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M Sani, ya jagoranci tawagar masu bincike zuwa wurin domin tantance abin da ya faru.

Sanarwar ta ce, “A yayin da ake ci gaba da bincike, mutum 47 daga cikinsu sun riga sun shiga hannu kuma nan gaba za a gurfanar da su a kotu.”