✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kama ’yan fashi 26 aka ƙwato wayoyin sata 126 a Kano

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kano ta kwato wayoyin sata 126ntate da kama masu fashin waya 26.

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Kano ta kwato wayoyin sata 126ntate da kama masu fashin waya 26.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kuma ƙwato miyagun ƙwayoyi da makamai da kwamfutocin laptop a hannun ’yan fashin.

Ya ce an kama ’yan fashin ne a kwanaki 12 na farkon watan nan na Satumba, 2024.

Ya ce an gudanar da aikin ne domin kakkaɓe ’yan fashin waya da dangoginsu da suka addabi al’ummar birnin Kano.

Kiyawa ya ce za a gurfanar da waɗanda aka kaman a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.

Wayoyin da sauran kayan satan kuma za a mayar wa masu su bayan an tantance su.