Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wadanda ake zargi da yin fashi a gidan saukar baqi na Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa da ke kan Titin Hadeja a birnin Kano.
Kakakin Rundunar, SP Magaji Musa Majiya ne ya bayyana haka a cikin wata takadar da ya sanya wa hannu tare da raba wa manema labarai a Kano.
Wadanda ake zargin sun hada da Nura Ahmed da Abdullahi Ahmed da Abubakar Uzairu wanda aka fi sani da Babayo, dukansu mazauna Titin Sultan ne da ke Unguwar Nasarawa Kano; kuma ana zarginsu ne da hada baki da wani korarren dan sanda da ya taba yin aikin gadi a gidan Mataimakin Gwamnan mai suna Saje Sani danjuma; suka yi fashi a ranar 18 ga Marsi din nan. A yayin fashin, an ce suna dauke da miyagun makamai kuma sun far ’yan sandan da ke gadin gidan, inda suka qwace musu bindiga qirar AK47, wacce ke cike da harsashe 30. Haka sun sace mota qirar BMb wacce qimarta ta kai Naira miliyan 11 baya ga wannan kuma sun kwashi kudi da ba a san yawansu ba.
SP Majiya ya qara da cewa jami’an yaqi da miyagun ayyuka ne (SARS) suka yi nasarar kama wadanda ake zargi da fashin, sakamakon umarnin da Kwamsihinan ’Yan sandan Jihar Kano, Rabi’u Yusuf ya bayar. Ya ce wadanda ake zargin sun jagoranci ’yan sanda zuwa maboyarsu, inda aka samo bindiga tare da motar da suka sace a gidan Mataimakin Gwamnan.
“Jami’anmu na ci gaba da gudanar da bincike don gano ragowar makaman wadanda ale zargi da fashin. Bayan haka kuma za mu gurfanar da su gaban kotun da ke da hurumin gudanar da shari’ar,” inji Majiya.