✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yan fashin da suka harbi babban jami’in ’yan sanda

Wasu gaggan ’yan fashi da makami da suka buɗe wuta a kan DPO na yankin Ogbere, CSP Adeyinka Akingbade a makon jiya sun shiga hannu.…

Wasu gaggan ’yan fashi da makami da suka buɗe wuta a kan DPO na yankin Ogbere, CSP Adeyinka Akingbade a makon jiya sun shiga hannu.

Lamarin ya faru ne bayan bayanan sirri da DPO ya samu na cewa ’yan fashin sun sauka a wani gidan saukar baƙi, kana suna shirin aiwatar da fashi a kan hanyar nan ta Jihar Benin daga Shagamu. Nan take DPO ya jagoranci tawagar ’yan sanda suka yi wa ɓarayin dirar mikiya, inda ya nemi su miƙa kansu amma sai babbansu mai suna Mangofak ya buɗe masa wuta suka tsere.

Ɗaya daga cikin ’yan fashin su biyu da aka kama mai suna Wasiu Ganiyu ya shaida wa Aminiya cewa jagoransu ne ya buɗe wa DPO wuta a lokacin da ya nemi su miƙa wuya. “Nan take Mangofak ya ɗauki bindiga da ke kan gado ya buɗe wa jami’in ’yan sandan wuta, nan take muka tsere. Mun biya ta wani gidan man fetur, inda muka yi fashi a wajen, sannan muka ƙwaci wata mota wacce muka shiga muka tsere; kafin daga bisani mu samu maɓoya a wani dajin da ke kan hanyar Benin, inda a nan ne jami’an ’yan sanda na SARS suka dirar mana bayan mun yi ba-ta-kashi da su. Sun kashe babbanmu Mongofak, suka kuma kame mu,” inji shi.

Wasiu ya shaida cewa sai da ya yi zaman kaso a gidan yari a Jihar Oyo har na tsawon shekaru 5 kafin daga bisani ya ƙara shiga wani ayarin ’yan fashin, shekara guda da fitowarsa daga kurkuku. Ya ce ya taɓa zama babban jigo a tawagar ƙasurgumin dan fashi mai suna Godogodo.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Ogun, ASP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa bayan harbe jami’in ɗan sandan da ’yan fashin suka yi ne sai Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ahamad Iliyasu ya bai wa jami’an ‘yan sanda na musamman da ake kira FSARS, a ƙarƙashin jagorancin  DSP Uba Adamu umarnin zaƙulo ’yan fashin cikin awa 24; inda suka lalubo maɓoyar ’yan fashin, inda suka share kimanin awa guda suna musayar wuta; abin da ya yi sanadiyyar kashe jagoran ’yan fashin tare da kame ragowar biyun.