✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yan damfara masu kwaikwayon muryar aljanu a Katsina

Suna kiran mutane ne a waya suna kwaikwayon muryar aljanu.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina ta samu nasarar cafke wani gungun ’yan damfara dake kwaikwayar muryar aljanu don su damfara mutane.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar SP Gambo Isah ne ya bayyana haka lokacin da ake holen bata-garin da rundunar ’yan sandan ta samu nasarar cafkewa a fadin jihar.

Ya kara da cewa, wanda ake zargin suna kiran mutane ne a waya tare kwaikwayar muryar aljanu dan cimma mugun nufinsu.

“Ababen zargin sun damfari wata mata mai suna Hajiya Jamila Naira dubu dari biyu da arba’in da bakwai  bayan sun kirata a waya sun nuna mata cewa su aljanu ne.

“Abba Iliyasu da Usman Adamu da Abdurauf Iliyasu wadanda ’yan asalin Jihar Kano ne sun umarci Hajiya Jamila wacce ke zaune a Jihar Katsina da taje bayan gari inda ta ringa tura musu kudi” a cewar Kakakin.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su tisa keyar wadanda ake zargi zuwa kotu.