Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7.
An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi.
- An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe
- Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin Zamba da ke Abuja, yayin da ta ukun da ake zargin ma’aikaciyar jinya ce da ta tsere a yanzu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Henry Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Okoye ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a Owerri, babban birnin jihar a ranar 14 ga watan Afrilu, biyo bayan wani samame da jami’an tsaro suka yi a lokacin da suke ƙoƙarin siyar da yaron kan kuɗi Naira miliyan 2.7.
Ya ce, an kama mutanen ne biyo bayan ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin rundunar ’yan sandan Jihar Imo da hedikwatar ’yan sandan shiyya ta 7 da ke Abuja, duk da cewa an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na shiyyar Abuja, domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.
Okoye ya ce, “Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta gano wani mutum da ake zargi da safarar ƙananan yara, lamarin da ya kai ga cafke wasu mata biyu da ake zargi tare da kuɓutar da wani yaro ɗan shekara huɗu.