✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wani fursunan Kuje a Kaduna

An kama fursunan yana shirin kama hanyar tafiya Jihar Kano.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar cafke daya daga cikin tserarrun fursunonin kurkukun Kuje yana shirin tafiya Jihar Kano.

A cewar ’yan sandan, an kama fursunan mai suna Ali Shu’aibu, da misalin karfe 7.30 na Yammacin ranar 17 ga wata Yulin da muke ciki.

Cikin sanarwar da jami’in hulda da al’umma na jihar, DSP Muhammed Jalige ya fitar, ya ce fursunan mai kimanin shekaru 60 dan asalin Jihar Kano ne wanda aka kama shi wani wuri a Kaduna.

DSP Jalige ya ce fursunan yana daya daga cikin wadanda suka tsere daga gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja, babban birnin kasar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Yekini A. Ayoku, ya ba da umarnin a yi duk wata mai yiwuwa gabanin mayar da fursunan inda ya fito.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu ’yan bindiga a ranar 5 ga watan Yuli suka kai hari gidan gyara halin na Kuje inda suka kubutar da daruruwan fursunoni ciki har da ’yan ta’addan Boko Haram.

Tun bayan kai harin ne Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali ta Najeriya NCoS, ta fitar da sunaye da fuskokin ’yan ta’adda 69 daga cikin fursunonin da take nema ruwa a jallo.