✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wani da ƙoƙon kan mutum a Abuja

Mutumin ya ce ya tsinci ƙoƙon kan ne da wasu sassa na ƙwarangwal ɗin mutum a daji lokacin da yake farauta.

Rundunar ’yan sandan Abuja ta ce jami’anta sun kama wani mai suna Nuhu Ezra ɗauke da ƙoƙon kan mutum.

Kwamishinan ’yan sanda CP Benneth Igweh ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin yi wa manema labarai holen mutumin jami’an ofishin ’yan sanda na Iddo suka kama a ranar Talata.

CP Igweh ya ce mutumin wanda ya fito daga ƙauyen Gosa Kipikipi ya shiga hannu ne bayan samun bayanan sirri, inda aka kama shi da ƙoƙon kan a ɓoye cikin buhu.

Aminiya ta ruwaito cewa yayin da mutumin da ake zargi ke amsa tambayoyi, ya ce ya tsinci ƙoƙon kan ne da wasu sassa na ƙwarangwal ɗin mutum a daji lokacin da yake farauta a Kuje tare da cewa yana shirin sayar da su kan N600,000.

Kwamishinan ’yan sandan ya bayar da umarnin ƙaddamar da bincike domin gano sassan jikin mamacin da kuma wanda ke shirin saye.

Sannan binciken zai tantance ko wanda ake zargi “ya kashe wani ne domin fataucin sassan jikinsa, a matsayin wata hanyar kasuwanci.”

CP Igweh ya buƙaci mazauna babban birnin ƙasar da su ci gaba da sanya idanun lura kan duk wani motsi da ke gudana tare da miƙa rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.