Daya daga cikin ’yan bindiga da suka kashe Nabeeha Al-Kadriyar, dalibar ajin karshe a Jami’ar Ahmadu (ABU) Zariya da sauran wadanda aka sace a Abuja.
Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, ya ce an dan bindigar mai mai shekaru 28 ne a Kaduna, da kudin da ake zargin kudin na fansa ne.
“Bayan samun bayanan sirri ne ’yan sanda suka ritsa shi a wani otal a yankin Tafa, inda suka kama shi da da kudi Naira miliyan 2.5 da ake zargin wani kaso ne na kudin fansa da suka karba.
“Shi da kansa ya shaida wa masu bincike cewa yana cikin gungun da suka sace iyalan wani lauya a yankin Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairu, 2024, suka kuma kashe wasu da aka yi garkuwa da su, ciki har da Nabeeha, a ranar 13 ga wata.
- Hanyoyi 5 na samun saukin tsadar rayuwa a Najeriya
- An yanke mazakutar malamin allo daf da aurensa a Zariya
“Wanda ake zargin ya yi kokarin ba wa DPOn Tafa da ya kama shi cin hancin Naira miliyan daya, amma DPO ya ki amincewa, kuma ya gudanar da aikinsa,” in ji sanarwar.
Adejobi, wanda ya ce ya ce a ranar 20 ga watan Janairu, 2024 aka kama dan bindigar, ya ce Shugaban yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga sashen DFI-IRT na rundunar da ke Abuja domin gudanar da bincike mai zurfi.
Ya kuma yaba wa DPOn Tafa, SP Idris Ibrahim, bisa jajircewa da kwarewar da ya nuna, sannan ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta raga wa masu aikata laifuka ba.
Aminiya ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka sace mutane daga rukunin gidaje na Sagwari da ke unguwar Dutsen-Alhaji a Karamar Hukumar Bwari da ke Abuja.
Masu garkuwa da mutanen sun kashe hudu daga cikinsu, ciki har da Nabeeha Al-Kadriyar, da kuma Folashade Ariyo mai shekara 13.
An sace Nabeeha ce tare da ’yan uwanta mata biyar da mahaifainsu daga gidansu da ke unguwar Zuma 1 a wajen garin Bwari a ranar 2 ga watan.