✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wadda ta daure danta tsawon shekaru a Kano

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wata mata mai suna Maryam Dauda bisa zarginta da daure danta mai kimanin shekara 12 a turke. An…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wata mata mai suna Maryam Dauda bisa zarginta da daure danta mai kimanin shekara 12 a turke.

An kamar matar ce da take zaune a Unguwar Liman a Dorayi Babba ta Karamar Hukumar Gwale a Jihar, inda dan nata yake kwance tsirara a cikin najasa har yana cin kashinsa.

Aminiya ta jiyo cewa, asirin matar ya tonu ne a lokacin da masu gidan da matar take haya suka yi niyyar sayar da gidan, inda aka kai wani da yake da niyyar saye don gane wa idanunsa yanayin gidan.

Malam Ibrahim Babanladi Satatima shi ne wanda ya je gidan inda ya gane wa idonsa halin da yaron yake ciki.

Ya shaida wa Aminiya cewa, “Lokacin da muka je gidan muna duba gidan sai muka ga yaron a jikin turke kamar dabba a cikin najasa kaca-kaca yana kuma cin kashin da ya yi.

“Kuma ga dukkan alamu yaron shi kadai ne a cikin gidan don sai daga baya mahaifiyarsa ta zo.”

A cewarsa hakan ya sa suka yi gaggawar sanar da ’yan sandan yankin inda suka zo suka kwashe su zuwa ofishinsu na Dorayi.

“Mun so mu yi magana da mutanen unguwar amma suka ki ba mu hadin kai, domin har gidan mai unguwa muka je ba mu samu ganinsa ba, inda aka gaya mana ba ya nan.

“Muka zauna muka jira shi muka kira wayarsa amma ba mu same shi ba, daga nan ne muka sanar da ’yan sanda don a zo a taimaka wa yaron tare da mahaifiyar tasa domin akwai alamun talauci a tare da ita.

Malama Maryam Dauda ta ce, talauci ne dalilin shigarsu wannan hali saboda babu wanda yake taimaka mata da abinci bayan da mahaifin yaron ya rasu.

Mahaifiyar yaron wanda ba a bayyana sunansa ba ta yi karin haske cewa, yaranta uku ne masu lalurar tabin hankali sai dai biyu daga ciki sun rasu yayin da wannan yaron ya rage.

Kwamared A. A Haruna Ayagi shi ne Shugaban Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ya ce, ba za su bar wannan lamari ba za su tabbatar an kwato wa yaron hakkinsa.

“Wannan wani nau’i ne na azabtar da yara don haka ba za mu bari ba. Za mu bibiyi lamarin har sai an binciki lamarin zuwa karshe.”

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, mahaifiyar yaron tana wurinsu da zarar an kammala bincike za a gurfanar da matar a gaban kotu.

Haka kuma DSP Kiyawa ya bayyana cewa, tuni jami’ansu suka kai yaron Asibitin Kwararru na Murtala domin samun kulawar gaggawa.