✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wadanda suka yi wa dan kasar Indiya fashi a Kano

An kama 'yan fashin a cikin gidan dan kasar Indiyar da ke Kano.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta cafke wasu mutum biyar da ake zargi da yi wa wani dan kasar Indiya fashi da makami a jihar.
Ana zargin mutanen da shiga gidan mutumin da ke unguwar Sharada a Karamar Hukumar Birni.

Da ya ke gabatar da masu laifin ga maneman labarai a Kano, kakakin ‘yan sandan Jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke su ne yayin wani sintiri.

“Tawagar ‘Puff Adder’ karkashin jagorancin SP Abdulrahim Adamu, ne suka gudanar da sintiri a yankin Sharada, Karamar Hukumar Birnin, sun tare wani babur mai kafa uku dauke da wani mutum guda daya a kofar gidan wani dan kasar Indiya.

“Da ganin ‘yan sandan, direban babur din mai suna Alhaji Musa mai shekara 45 da ke Tudun Rubudi a Kano, ya yi yunkurin tserewa, amma tawagar ta harbi tayar babur din, An cafke wani mai suna Onyekachi Jude mai shekara 19 da ke yankin Rinji a Kano.

Kiyawa ya kara da cewa an kama wasu a cikin gidan dan kasar Indiyar yayin da suke masa fashi.

“Harbin bindigar da ’yan sanda suka yi, ya ja hankalin ‘yan fashin da ke cikin gidan dan kasar Indiyar, wanda suka yi kokarin tserewa,tuni aka kama mutum uku a cikin gidan.

“An samu wayar hannu, Kwamfuta, waya kirar iPhone da kuma kudaden kasar Indiya,” a cewarsa.

A cewarsa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu don gudanar da bincike.