✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wadanda suka kashe sufeton ‘yan sanda

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kurosriba ta kama wasu manyan da ake zargi da aikata laifi, cikinsu har da wasu mutum takwas da aka zarga…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kurosriba ta kama wasu manyan da ake zargi da aikata laifi, cikinsu har da wasu mutum takwas da aka zarga da kashe wani Sufeton ’yan sanda da ke aiki da rundunar ’yan sanda a Jihar Enugu mai suna Micheal James, lokacin da ya zo hutun karshen shekara.

Binciken Aminiya ya gano cewa wani dan sanda da ya bar aiki, Dominic Umoh tare da wasu mutum shida ne suka yi wa wancan dan sanda kwanton bauna sa’ilin da ya je wani gidan mai da nufin sayen mai a kauyen Ojor da ke yankin Uyanga, karamar Hukumar Akamkpa suka kashe shi, suka datse kansa suka kai gidan tsafinsu; gangar jikin kuma har yanzu ba a ganta ba. Bayan matasan sun kashe shi sai kuma suka kona motarsa kirar Sienna, suka kuma dauke karamar bindigarsa.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da nasarorin da rundunarsa ta samu tun daga lokacin da aka turo shi jihar Kurosriba aiki, Kwamishinan ’yan sanda Hafiz Muhammad Inuwa ya ce daga lokacin zuwa wannan wata na Janairu 2018, “rundunar ta kama ’yan fashi da makami 186, yayin da ta kama wadanda ake zargi da kisan kai su 83. Sauran wadanda aka kama su ne ’yan fashi kan teku su 5 sai kuma wadanda suka yi yunkurin kisan kai su 9. Akwai kuma masu fyade su 21,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa: “Mun kama masu yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa mutum 40, masu sata da kuma hada baki 29, mallakar makami ba bisa ka’ida ba, an samu mutum 80 sai kuma ’yan kungiyar asiri mutum 60 aka kama. An ma samu masu bata kananan yara mutum 4, zamba cikin aminci da zubar da ciki ba bisa ka’ida ba mutum 3, masu kwace, an samu mutum 1. Kana kuma mun kwato makamai a hannun bata gari har guda 234. Gaba daya dai kimanin mutum 529 muka yi katarin kamawa bisa zargin aikata laifuka da aka ambata.”

Ya jinjina wa jami’an nasa bisa mayar da himma kan aiki da kuma jajircewa.

Ya kara da jan kunnen duk wani wanda ya san yana aikata abin da bai dace ba, da ya yi karatun-ta-natsu domin har aba da rundunarsa ba za ta saurara wa duk wani takadari ko takadara ba. Ya ce wadannan da aka gabatar wa ’yan jarida duk kotu za a mika su da zarar an gama bincikensu.