Jami’an bijilanti a yankin Unguwa Uku ’Yan Awaki a Jihar Kano sun samu nasarar kama wasu matasa guda biyu da ake zarginsu da satar kofofin gidaje da shagunan mutane.
Matasan da ake zargi dukkan su mazauna unguwar Kureken Sani ne da ke Karamar Hukumar Kumbotso, kuma ’yan bijilantin da ke karkashin jagorancin Adamu Abubakar Fiya-Fiya ne suka kama su.
Matasan sun amsa cewa kofar da suka sace ranar da dubunsu ta cika ta wani gida ce suka cire.
Sai dai sun nemi a yi musu afuwa kan laifin da suka aikata.
A nasa bangaren, Kwamandan bijilantin na Unguwa Uku ’Yan Awaki, Adamu Abubakar Fiya-fiya ya ce da zarar sun kammala bincike za su mika su ga ’yan sanda domin fadada bincike a kansu.
“Wadannan matasan ana zargin su ne da sata da rana sai su shiga gidan mutane, ko kuma kangwaye su balle kofofin da aka sanya, kuma Allah Ya ba mu nasara muka kama su a wannan wata na Ramadana,” in ji Kwamandan.
A karshe ya yi kira ga jama’a da su rika sanya idanu a kan duk wani motsin da ba su amince da shi ba sannan su sanar da jami’an tsaro mafi kusa don kawo daukin gaggawa.