✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama uwa ta sayar da jaririnta N150,000

'Yan sanda sun yi nasarar ceto jaririn bayan uwarshi ta sayar da shi N150,000.

’Yan sandan sun cafke wata mata, mai shekara 21 a duniya, bisa zargin sayar da jaririnta mai wata uku a haihuwa a kan N150,000.

Kakakin ’yan sandan Jihar Anambra, inda aka kama matar ya ce wadda aka zargin ta fito daga kauyen Ire-Ojoto na Jihar Akwa Ibom.

“Bayan gudanar da bincike an gano matar ta yi yunkurin sayar da jaririn mai wata uku a duniya nesaboda shiga matsanancin hali da ta yi.

“An ceto jaririn kuma yana cikin koshin lafiya, za a ci gaba da bincike don gano dalilinta na yin haka”, cewar Haruna.

Wannan ba shi ne karon farko da aka samu uwa na shirin sayar da jaririn da ta haifa ba.

Wasu na fakewa da cewa talauci da wahalar rayuwa ce ke tilasta su yin hakan.