An kama wata mata da ake zargin ta da rataye wani yaro mai shekaru biyu a haihuwa a Jihar Katsina.
An zargin matatar mai shekaru 35 da yin wannan aika-aika ne a unguwar Lungun Loma da ke yankin Ƙaramar Hukumar Dutsinma.
Matar ta yi yaron wanann aika-aika ne ta hayar ɗaure shi da zane ta kuma rufe shi a cikin ɗaki tayi tafiyar ta.
Matar wadda a jawabin ta ta ce, ba ɗaure yaron ta yi ba, rufe shi kawai ta yi a cikin ɗakin, ta bayyana cewa ba ta san yadda aka yi har hakan ta faru ba.
- ’Yan ta’adda sun harbi shugaban rundunar tsaron al’ummar Zamfara
- An jefa yarinya a rijiya bayan yi mata fyaɗe
A cewarta, “Zan fita ne gudun kada ya biyo ni bayan na aza sanwa ga wuta, shi ya sa na rufe shi acikin ɗakin”.
Sai dai ba ta yi cikakken bayani a kan dalilin da ya sa ba ta tafi da shi inda za ta ba.
Matar ta ci gaba da cewa, sai bayan tana can waje sai ta ji ana cewa ta zo ana neman ta a kan cewa ta rufe yaro bayan ta ɗaure shi acikin ɗaki.
Ta shaida wa wakilinmu cewa yaron ɗan riƙonta ne, ba ita ce ta haifi yaron ba, kuma kyauta suke zama ɗakin da suke zaune a gidan da suke.
Bayanin wannan labarin ya fito daga wata ’yar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam mai suna Halima Aliyu wadda ta je aiki a unguwar inda ta fara jin raɗe-raɗin abin da ke faruwa a gidan.
Daga nan Halima ta kai rahoto ga rundunar ’yan sanda da ke Dutsinma, inda jami’anta suka je aka kai yaron asibiti domin duba lafiyar shi.
Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai inda ya ce, da zarar sun kammala bincike za su tura zuwa kotu.