Dubun wani sojan bogi ta cika bayan da aka kama shi da wayar wata mata da aka sace.
Kwamishinar ’Yan Sandan Jihar Oyo, Ngozi Onadeko, ta ce dubun matashin mai shekara 33 ta cika ne a garin Ogbomosho da ke jihar a yayin yake gabatar da kansa a matsahin soja.
- An kama dan kasar waje yana garkuwa da mutane a Najeriya
- Zan iya kwada wa saurayina mari a kan ‘bestie’ — Budurwa
“A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin satar da ake tuhumar shi da aikatawa, kuma yana amfani da kayan sojojin ne domin kada asirinsa ya tonu idan ya aikata laifi; Amma har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike,” inji ta.
Kwamishinar ’Yan Sandan ta ce matashin ya saba gabatar da kansa ga mutane a matasyin soja, kuma ko da ’yan sanda suka je gidansa suka gudanar da bincike, sun samu kakin sojoji kala biyu, rigar sanyin sojoji, marikin karamar bindiga, rigar ruwan sojoji da dai sauransu.
Amma a nasa bangaren, matashin ya ce sayen wayar da ake zargin ya sace ya yi, “Bayan ’yan sanda sun kama ni, na nemi su bi ni zuwa wurin da na saye ta amma suka ki.
“Da suka bincika wayar ce suka ga wani hoto da na dauka sanye da kayan sojoji, suka tambaye ni game da kayan, na shaida musu cewa na wani abokina ne da ke aikin soja a Jihar Borno.
“Daga nan sai suka kai ni gidana inda suka samu sauran kakin sojojin. Ni hoto kawai na dauka da kakin, na kuma ba su lambar wayar abokin nawa, su kira shi su ji.”
A cewarsa, “Yanzu wata takwas ke nan ina amfani da wayar da ake zargi, ni ban taba sanin cewa ta sata ba ce, na saye ta ne a wurin wani.”