✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama shi yana sayar da garin katako a matsayin maganin gargajiya

Ya hada siminti da garin katako yana sayarwa a matsayin magajin gargajiya

An cafke wani mutum da ke sayar wa mutane da garin katako da siminti a matsayin maganin gargajiya na cutar zazzabin cizon sauro.

’Yan sanda sun gano cewa mutumin yana hada garin katako da garin farin simintin POP a yana sayar wa mutane a matsayin garin maganin gargajiya.

A wani bidiyon da aka yi wa mutumin bayan ya shiga hannu, an ji shi yana cewa “Garin katako nake hadawa da garin siminti da kuma garin gypsum da ake yin POP da shi nake kulla a leda ina sayar wa mutane a matsayin maganin cutar maleriya da sauran cututtuka.

“Ina zuwa kasuwanni daban-daban ina sayarwa kuma mutane suna yawan saya.

“Ba ni da kayyadajjen farashin da nake sayarwa, kawai ya danganci yadda ciniki ya kaya.

“Na san yana da hadari, amma saboda yanayin matsayin rayuwar da kasa ke ciki shi ya sa nake yi.”

Wata mata mai suna Taibat, da ke zaune a unguwar Gerewu, ta ce wanda ake zargin yana yawan zuwa Kasuwar Mandate da ke Ilori yana sayar da garin, kafin dubunsa ta cika.

Taibat, ta yi kira ga jama’a su kara lura, sanna ta bukaci gwamnati ta dauki kwararan matakai, tana mai cewa Allah Kadai Ya san irin lahanin da garin ya yi mutanen da suka yi amfani da shi.

Wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, amma ya ce ba shi da labari.

Amma duk da haka, kakakin ’yan sandan ya ce zarar an sanar da ’yan sanda za su dauki mataki.