An damke wani matashi bisa zargin yin fyade ga wata yarinya ’yar shekara biyu a Jimeta, Jihar Adamawa.
’Yan sanda sun kama matashin ne bayan ya lalata yarinyar a ranar Talata 28 ga watan Yuli, a yankin Jambuttu Aso Rock, inji Kakakin Runduyar ’yan sandan jihar, Suleiman Nguroje.
“Matashin da kantinsa ke makwabtaka da na mahaifiyar yarinyar ya fake kamar yana kula da yarinyar, inda ya je ya lalata ta a wata makarantar firamare.
“Da mahaifiyar yarinyar ta lura cewa al’aurar diyarta ta kumbura sai ta yi hanzarin sanar da ’yan sanda suka tsare shi.
“Yanzu ana duba lafiyar yariyar, shi kuma an tsare shi ana ci gaba da bincikar sa”, inji shi.