An kama wani matsayi dauke kokon kawunan mutane takwas a Jihar Ondo.
Rundunar ’yan sanda a jihar ta ce ta yi nasarar kama mutumin dauke da kokon kawunan mutane takwas ne a lokacin da yake kokarin mika su ga bokaye.
Da yake nuna mutumin a wajen taro da ’yan jarida a ofishinsa a Akure, fadar jihar, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ondo, Abayomi Oladipo, ya ce, an kama mutumin ne a garin Isua-Akoko da ke Karamar Hukumar Akoko ta Gabas.
Ya ce ’yan sandan da ke aikin sintiri a kan hanyar Isua zuwa Ipinmi ne suka kama shi cikin wata mota kirar Nissan dauke da kokon kawunan mutane takwas da ya cunkusa su cikin buhun garin kwaki domin badda-kama.
- NAJERIYA A YAU: ‘Kananan Hukumomi Na Daf Da Zama Mabarata’
- A tanadi tsaro na musamman albarkacin bikin Sallah a Kano — Sarki Aminu Bayero
Da yake karin haske, kwamishinan ’yan sandan ya ce mutumin mai shekaru 37 ya furta da bakinsa cewa yana samun kokon kawunan mutane ne daga hannun wani mai suna Ismaila mazaunin Oboroku a garin Okene a Jihar Kogi.
Ya yi ikirarin cewa yana sayen kowane kokon kai guda daya a kan Naira dubu 30 zuwa 35.
Kuma a lokacin da aka kama shi ya tabbatar da cewa yana kan hanyar zuwa Osogbo a Jihar Osun ne domin sayar da wadannan kokon kawuna ga wasu bokaye.
Ya ambaci sunayen bokayen da ya saba kai wa kokon kai suna saya daga hannunsa.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce an kammala shirin mika wannan mutumi da kokon kawunan da aka samu a tare da shi zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) da ke Akure domin ci gaba da binciken lamarin.