✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama sassan jikin mutane da masu garkuwa a Adamawa

‘Yan sandan jihar Adamawa sun kame masu garkuwa da mutane 33 da barayi goma da ‘yan kungiyar asiri da sassan jikin mutane a kananan hukumomin…

‘Yan sandan jihar Adamawa sun kame masu garkuwa da mutane 33 da barayi goma da ‘yan kungiyar asiri da sassan jikin mutane a kananan hukumomin Maiha da Gombi da Mubi da kuma Fufore.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olugbenga Adeyanju ya ce rundunar ta kuma kama masu tayar da rikice-rikicen kabilanci goma 16 a jihar.

“Rundunar ta yi nasarar kame dan shekara 28 da wani dan shekara 36 da aka kama su dauke da sassan jikin mutane. Mun yi nasarar kame masu laifukan ne da hadin kai daga ‘yan banga”, inji shi.

Ya ce sun kuma kwace bindiga kirar AK47 da wadansu kananan bindigogi biyu da harbi-ruga guda daya da harsasai 322 da sassan jikin mutane.

Mutum 16 masu haddasa rikicin kabilancin kuma an kame su ne da makamai bayan sun haddasa rikici tsakanin kabilun Lunguda da Waja dake kananan hukuman Guyuk da Lamurde.