✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mutum daya da ake zargi da kai wa Soludo hari

Wanda ake zargi da hannu a kai harin ya shiga komar 'yan sanda.

A daren Laraba da ya gabata ne rundunar ‘yan sanda a Jihar Anambra, ta cafke wani mutum da ake zargi yana daya daga cikin wadanda suka kai wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya hari.

Kakakin ‘yan sandan Jihar Ikenganya Tochukwu ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan a ranar Alhamis.

Charles Soludo, wanda zai yi takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APGA a zaben Jihar Anambra mai zuwa, ya yi gamo da ‘yan bindiga wanda suka kai masa hari a ranar Talata inda suka kashe mutum uku daga jami’an tsaronsa.

Ya ce, “Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Monday Bala Kuryas, ya jajantawa tsohon Gwamnan Babban Bankin da kuma iyalan wadanda suka rasu a yayin harin,” a cewar Tochukwu.

Bayan kai harin ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da Kwamishinan Ruwa da Albarkatu na jihar, Injiniya Emeka Ezenwanne.

Kazalika, Tochukwu ya ce jami’an tsaro sun ziyarci gidan Soludo inda suka jajanta masa tare da ba sa karin jami’an tsaro don ba shi kulawa.

Bayan ziyara gani da ido da Kwamishinan ‘yan sandan ya kai wajen da harin ya faru, ya yi alkawarin tabbatar da kama wadanda masu hannu a harin cikin kankanin lokaci.

Ya kuma ja hankalin mutanen jihar da su hada hannu da jami’an ‘yan sanda wajen yakar ta’addanci a jihar.

A nasa bangaren, Soludo ya yi godiya da jinjina ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar kan yadda suka kai masa dauki a lokacin da harin ya faru.