✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mutum 84 kan zargin yi wa mata 8 fyade a Afirka ta Kudu

An yi musu fyaden ne a wajen wani raye-raye

A Afirka ta Kudu, an gurfanar da mutum 84 da aka kama bisa zargin yi wa wasu mata su takwas fyade lokaci daya a wani wajen daukar bidiyon raye-raye.

An gurfanar da mutanen ne a gaban kotu ranar Litinin, a wani abu da Ministan Harkokin ’Yan Sandan kasar, Bheki Cele, ha bayyana a matsayin abin kunya ga kasar.

A ranar Alhamis ce dai wani gungun ’yan bindiga ya kutsa kai wani wajen da ake daukar bidiyon waka kusa da wani wajen hakar ma’adinai a garin Krugersdorp da ke Yammacin Johannesburg ranar Alhamis.

A wajen dai an yi wa matan takwas fyade a yanayin da ya girgiza kasar, kuma yana daya daga cikin irinsa mafi muni a duniya.

A cewar Ministan ’yan sandan lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin, “Abin da ya faru a Krugersdorp abin kunya ne ga kasa baki daya.

“Wasu daga cikin wadannan matan za su jima suna fama da tabon abin a jikinsu tsawon lokaci,” inji shi.

’Yan sanda dai sun zargi ’yan ci-ranin da ke hakar ma’adinai da ake kira ‘Zama-zama’ da hannu a aika-aikar, sannan suka kama mutum 84 a wani samame a yankin.

Kazalika, an kuma kashe mutum biyu yayin wata musayar wuta da ’yan sanda, na ukun kuma aka ji masa rauni kuma tuni aka garzaya da shi asibiti.

Shugaban ’yan sandan kasar dai ya ce za a gudanar da cikakken bincike don gano ko mutanen da aka kama suna da hannu a fyaden ko kuma a’a.