’Yan sandan sun cafke mutum 54 da ake zargi da aikata manyan laifuka a Jihar Edo.
Hakan ya fito me daga bakin kakakin ’yan sandan jihar, SP Kongtons Bello, inda ya ce ana zargin mutanen da aikata fashi da makami, garkuwa da mutane, fyade da sauransu.
- Limamin coci ya raba wa Musulmi Shinkafar Sallah
- Amarya ta fasa aure saboda ango ya fadi jarabawar lissafi
- Ba za a yi Hawan Sallah ba a Katsina da Daura
- Bikin Sallah: Za a girke jami’an tsaro 5,350 a Kwara
Bello, ya kara da cewa dubun mutanen ta cika ne yayin da rundunar ’yan sandan jihar ta baza koma tare da nasarar kamo su.
Kazalika, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Philip Ogbadu, ya ba wa jama’ar jihar tabbacin ci gaba da farautar bata-gari, har sai ya dakushe daga jihar baki daya.
Daga wanda dubun tasu ta cika, akwai wanda ya kware wajen kwacen mota a Benin, babban birnin jihar.
Wanda ya kware wajen kwacen motar, kuma ya amsa cewar ya jima yana sheke ayarsa kafin dubunsa ta cika.