✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 523 kan satar mutane da ƙwacen waya a Kaduna

Mutane 532 sun shiga hannu kan zargin garkuwa da mutane da ƙwacen waya da kuma fashi da makami, inda aka ƙwato muggan makamai da dukiyoyin…

Dubun mutane 523 ta cika kan zargin garkuwa da mutane da fashin waya da sauran laifuffuka a Jihar Kaduna.

Mutum 350 daga cikin waɗanda ake zargin, an kama su ne a sakamakon samamen da ’yan sanda a suka kai matattaran ɓata-gari a sassan jihar.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce mutanen da aka kama sun haɗa da masu garkuwa da mutane 26 da masu fashin waya 97 da masu ƙwacen mota 17 da ɓarayin shanu 12 da masu aikata fyaɗe 10 da sauransu.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kaduna, Ibrahim Abdullahi ya ce an ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda biyar da Pistol biyu da mai sarrafa kanta (SMG) ɗaya da harsasai 102 da kuma shanu 283 da tumaki 20 daga hannun ɓata-garin da suka shiga hannu.