✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 5 kan zargin datse kan karuwa don yin tsafi

Sun dai yaudareta ne a matsayin za su yi amfani da ita kafin su datse mata kan

Akalla mutum biyar ne ’yan sanda suka kama a Jihar Kwara kan zargin kashe wata karuwa mai suna Abigail da kuma datse mata kai don yin tsafi.

Kakakin rundunar a Jihar, Ajayi Okasanmi ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Samuel Peter Tsado ne ya yaudareta a matsayin ya zo amfani da ita.

Ya kara da cewa daga bisani, Samuel tare da taimakon wani abokinsa mai suna Mohammed Gbara sun kasheta.

Kakakin ya ce sauran masu hannu a tabargazar sun hada da Abubakar Mohammed da aka fi sani da Mallam Baba Pati da Mohammed Ahmadu da kuma Bala Karim.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, Ajayi ya ce, “An datse kan Abigail ne da wuka sannan aka jefar da gangar jikinta a wani daji da ke kan hanyar Patigi zuwa Rufin.

“Sai dai bincike ya kai ga kama Samuel, wanda ya amsa cewa ya yaudari karuwar ne a matsayin zai yi amfani da ita, alhalin a zahiri so yake ya yi tsafi da ita,” inji shi.

Ya ce kama wadanda ake zargin ne a birnin Minna ya sa suka shiga daji domin dauko gangar jikin Abigail din.

“Da Samuel din da Mohammed kowa kama gabansa ya yi, sai daga bisani suka sake haduwa a garin Bida, inda a can ne suka ajiye kan nata a hannun wani Mohammed Abubakar, suna jiran zuwan wasu matsafa daga Jihar Borno, domin hada tsafin yin kudi.

“Sun amsa laifin da kuma na yanke hannun wani wanda har yanzu ba kai ga tantance wane ne ba,” inji shi.

Kakakin ya ce har yanzu rundunar na kokarin gano kan karuwar da ke hannun wanda ake zargin da kuma wasu mutum uku da har yanzu ba su shiga hannu ba.