✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 3 kan kashe malamin makaranta a Legas

Ana zargin mutanen da yi wa malamin dukan kawo wuka har ya yi ajalinsa.

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Legas sun cafke wasu mutum uku da ake zargi da kashe wani malamin makaranta.

Marigayin mai suna Idowu Hamzat wanda ke zaune a garin Ibadan a Jihar Oyo, ana zargin cewa mutane ukun ne suka kashe shi.

Wadanda ake zargin sun yi wa mamacin dukan tsiya har ya mutu a kan wani lamari da ba a bayyana ba.

Yanzu haka dai jami’an ‘yan sanda na binciken wadanda ake zargin sun yi wa malamin mai shekara 36 dukan kawo wuka har lahira.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, ya kuma kara da cewa an garzaya da su zuwa sashen binciken laifin kisan kai na rundunar ‘yan sandan jihar.