✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An kama mutum 3 da suka yi yunkurin sace ubangidansu

Ba mu ji dadin korar da ya yi mana daga aiki ba.

‘Yan sanda a Jihar Ogun sun damke wasu mutum uku bisa zargin yunkurin yin garkuwa da wani tsohon ubangidansu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya ba da bayanin haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata.

Ya ce wadanda ake zargin sun shiga hannu ne bayan da wani mai suna Ifenuga Olayinka ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda da ke Igbeba yana mai cewa ya samu sakon tes a wayarsa daga wani da ya kira kansa da “Killer Vagabond of Africa”.

Ya ce mutum da ya kira shi ya yi masa barazanar ya tura kudi Naira miliyan biyar cikin asusun bankin da aka tura masa lambar, ko kuma a garkuwa da shi.

Jami’in ya ce ganin haka ya sa aka baza jami’ai don binciko wadanda ke da hannu a barazanar.

Ya kara da cewa, an yi nasarar cafke biyu daga wadanda ake zargin ne a Jihar Anambra bayan da aka zurfafa bincike.

Kana daga bisani aka kamo na ukunsu a yankin Ago Iwoye.

Ya ce, bayan da aka gabatar da su ga wanda ya kai rahoton sai ya gano ashe tsoffin ma’aikatansa ne wadanda ya kore su daga aiki ba da dadewa ba saboda rashin da’a.

Da suke maida jawabi, wadanda ake zargin sun amsa tuhumar, tare da cewa sun yi yinkurin garkuwa da tsohon maigidan nasu ne saboda ba su ji dadin korar da ya yi musu ba.

Tuni dai Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Lanre Bankole, ya ba da umarnin a mika wadanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar don zurfafa bincike.