✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mutum 19 bisa zargin garkuwa da mutane a Jigawa

An kama su ne maboyarsu da ke Kananan Hukumomin Ringim da Garki.

Rundunar ’yan sanda ta Jihar Jigawa ta tabbatar da kama mutum 19 da take zargi da hannu a garkuwa da mutane a Jihar.

Kakakin rundunar, ASP Lawan Shi’isu ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa a Dutse, babban birnin Jihar ranar Talata.

Ya ce ayarin jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda da kuma wasu masu aikin sa-kai da aka fi sani da ’Yan Bulala ne suka kama wadandsa ake zargin, karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Aliyu Sale.

ASP Lawan ya ce an kama su ne ranar Litinin bayan rundunar ta kai wani samame kan maboyarsu da ke Kananan Hukumomin Ringim da Garki na Jihar.

A cewarsa, an kama su ne a yankunan da gudunmawar ’Yan Bulala da ke karkashin jagorancin CP AS Tafida, da tallafin Baturen ’Yan Sanda na Ringim a maboyarsu da ke kauyen Galaga a Karamar Hukumar Ringim da kuma dajin Fagen Gawo da ke Karamar Hukumar Garki.

“Uku daga cikinsu an kama su ne a Galaga, 16 kuma a Fagen Gawo,” inji Kakakin.

Kazalika, ya ce an kuma sami nasarar kwace makamai kamar su kwari da baka da adda da wuka da wayoyin salula biyu da layukan waya da guru da sauran kayan tsafi da dama a hannunsu.

Ya ce ko a ranar hudu ga watan Satumba da misalin karfe 4:00 na yamma sai da wasu masu garkuwar dauke da makamai suka dauke wani Alhaji Kabiru Ahmed mai kimanin shekara 60 a gidansa da ke Karamar Hukumar Taura.

Rahotanni dai sun ce har yanzu ba a san inda masu garkuwar suka kai shi ba, ko da yake ’yan sandan sun ce suna ci gaba da bincike a kai.

%d bloggers like this: