’Yan sanda a jihar Borno sun kama wasu da ake zargin suna lalata gadar sama da ke Maiduguri babban birnin Jihar.
ASP Nahum Daso Kenneth, Kakakin rundunar a Jihar ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri.
- An jikkata mutane da dama a rikicin makiyaya da manoma a Kano
- Kujerar Gwamnan Kano: Za mu garzaya Kotun Koli – Abba
A cewar Daso, an kama wadanda ake zargin ne a yayin da suke lalata gadar, tare da ajiye ginshikan da kuma cire sassanta don wata manufasu ta daban.
Ya ce an kama wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifin tare da wasu mutane biyu da su ma suka shiga aikata laifin wadanda yanzu suke komar ’yan sandan.
Ya kara da cewa sukan sayar da kayayyakin sata da aka fi sani da ‘Ajakuta’, lamarin da gwamnatin jihar ta sanya wa dokar hana amfani da su a fadin Jihar.
A baya dai Gwamnan jihar Babagana Zulum, ya sanya dokar hana ayyukan jari bola ne bayan ziyarar da ya kai Bulumkutu inda aka kwashe kadarorin gwamnati a rika sayar da su.
Daso ya ce dangane da haramcin da Gwamnan ta yi, ’yan sanda sun damke tireloli hudu da motar daukar kaya daya makil da karafa da aka lalata.
Ya ce motocin da aka kama na cike da kayayyaki da suka hada da motocin da suka lalace, da tarkacen karafa da sauran kayayyakin da suke zarfin sato su aka yi.
Ya ce an tuni rundunar ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya don girbar abin da suka shuka.