An kama mutum 107 da ke karbar horon aikin soji a wani sansanin sojoji na bogi da aka gano a Jihar Legas.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, ta ce shugaban sansanin sojin ruwan na bogi da ke yankin Ogudu a jihar ya shiga hannu kuma an kwace kayayyakin soji da dama a sansanin.
- Dan bindiga ya tona ’yan siyasar da ke daukar nauyinsu
- Najeriya A Yau: Yadda Abubakar Shekau ya yi kuruciyarsa
Da yake gabatar da mutanen da aka kama, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya ce kayan aka kwace daga hannunsu sun hada da kakin sojoji da katin shaidar aikin soji na bogi.
Sauran sun hada da takardun shaidar daukar aikin soji, takardun karin matsayi, bajen sojoji da mukaman sojoji da sauransu, duk na bogi.
Ya ce shugaban sansanin da ke kiran kansa mai mukamin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa, mai suna Sunday Dakare, na ikirarin cewa suna daukar jami’an sojin ruwa masu zaman kansu (Nigeria Merchant Navy) ne, wanda tuni Gwamnatin Tarayya ta haramta.
“Wannan babbar barazana ce ga kasarmu da zaman lafiyarta, musamman ma jihar; Wajibinmu ne mu tabbtar da dokar da ta haramta ayyukan irin wadannan haramtattun sansanonin soji.
“Ina kuma umartar duk masu irin wadannan cibiyoyi da ke aiki a jihar nan da su gaggauta rufe su,” inji shi.