✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutane 81 yayin zanga-zanga a Sakkwato

Kwamishinan ya ce jama’a na da damar su yi zanga-zangar lumana

Rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta sanar da cafke wasu mutum 81 da suka karya doka yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a jiya Alhamis.

Da yake tabbatar da hakan, kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Hayatu ya sanar cewa za su ci gaba da bai wa mutanen jihar tsaro a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar.

A bayanin da jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i ya fiyar ya ce kwamishina ya jinjina wa dukkan jami’an tsaron jihar kan hadin kan da aka samu na aiki tare a wannan lokaci mai cike da kalubale.

ASP Rufa’i ya ce hadin kan da aka samu tsakanin jami’an tsaron ne ya sanya aka samu nasarar kama matasan 81 da suka saba doka.

Ya bayyana cewa a yayin da wasu ke gudanar da zanga-zangar cikin lumana, an samu wasu da suka shiga far wa kayan gwamnati suna lalata su.

Ya ce wannan lamarin ya sanya jami’an tsaro suka dauki matakin tabbatar da an kiyaye doka da oda a yayin da wasu bata-gari suka yi yunkuri farfasa shagunan mutane.

Kwamishinan ya ce jama’a na da damar su yi zanga-zangar lumana, amma duk wanda ya yi amfani da damar ya barnata kayan gwamnati ko kawo tashin hankali hukuma za ta kama shi domin a hukunta shi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an gudanar da zanga-zangar lumana a kananan hukumomin Isa da Goronyo ba tare da samu wata hatsaniya ba.