Wani matashi mai shekara 25 mai suna Yunusa Haruna ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda da laifin daɓa wa yayansa wuƙa har lahira a ƙauyen Bakin Turu da ke ƙaramar Hukumar Shanga a Jihar Kebbi.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya yi amfani da wuƙa wajen daɓa wa yayansa, Isiyaku Haruna wuƙa a ƙirji wanda ya yi sanadin mutuwarsa.
- Za mu shirya Kwankwaso da Ganduje — Kofa
- Harin jirgin soji a Zamfara: Ya kamata a biya mu diyya —Iyalai
“An samu sahihan bayanai cewa, rukunin jami’an ’yan sandan da ke aiki a hedikwatar ’yan sanda ta Shanga ta kama wanda ake zargin,” cewar jami’an.
A wani rahoton kuma, wani Abubakar Umar mai shekara 25 a unguwar Jarkasa da ke ƙaramar hukumar Zuru ta jihar ya daɓa wa wani Mohammed Bala wuƙa mai kaifi a kan wata gardama, lamarin da ya yi ajalinsa nan take.
Ya kuma ƙara da cewa, wanda ake zargin ya kuma raunata ƙanin marigayin mai suna Sama’ila Bala.
“Bayan samun rahoton, rukunin ‘yan sandan da ke aiki a hedikwatar ‘yan sanda da ke Zuru, ta kai ɗauki tare da cafke wanda ake zargin,” in ji sanarwar.
Game da wannan batu, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kebbi, CP Bello M Sani, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi masu son zaman lafiya da su riƙa kai ƙorafinsu ga hukumomin da suka dace domin magance su, maimakon ace sun ɗauki hukunci a hannunsu.