✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe mahaifinsa a Kano

Hukumar Sibil Difens ta kama wani matashi dan shekara 25 kan daba wa mahaifinsa wuka ya kashe shi a Jihar Kano.

Hukumar Sibil Difens ta kama wani matashi dan shekara 25 kan daba wa mahaifinsa wuka ya kashe shi a unguwar Tudun Yola ‘C’, da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Kwamandan hukumar, Mohammed Falala ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda “marigayin, Alhaji Ya’u Mohammed, ya kawo dansa mai tabin hankali asibitin ƙwaƙwalwa da ke Dawanau, domin jinya daga Katsina, inda aka ba su lokacin ganin likita a ranar Asabar 6 ga watan Janairu.

“Maimakon komawa Katsina, sai marigayin ya yanke shawarar kwana a gidan dan uwansa a Tudun Yola.

“Binciken da muka yi ya nuna cewa ɗan nasa ya samu tabin hankali ne sakamakon ta’ammali da miyagun kwayoyi.

“A lokacin da suka isa Tudun Yola, sai mara lafiyar ya dauki wani abu mai kaifi ya soja wa mahaifin, har sai da jami’an NSCD suka zo suka kai mahaifin asibiti suka kama wanda ake zargin,” inji shi.

Falala ya ce tuni ’yan uwa suka yi shirin kai gawar Katsina domin yi mata jana’iza, yayin da aka mika wanda ake zargin ga ofishin ’yan sanda na Rijiyar Zaki domin ci gaba da bincike.