✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matashin da ake zargi da yi wa jaririyar wata 9 fyade a Legas

Ya yi aika-aikar ne lokacin da mahaifiyar jaririyar ta ajiye ta da nufin yin sayayya

’Yan sanda a Jihar Legas sun kama wani matashi mai shekara 27 wanda ake zargi da ya yi wa jaririyar wata tara a duniya fyade.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da kamun ranar Laraba.

Ya ce wani mutum ne ya kai wa ’yan sanda korafin aikata fyaden wajen misalin karfe 10:00 na daren Litinin.

Benjamin ya ce wanda ake zargin ya shiga gidan da mahaifiyar jaririyar ta shimfidar da ita a kasa, ta fita domin yin sayayya a waje.

Kakakin ya ce, “Ana zargin a nan ne mutumin ya yi wa jaririyar fyade sannan ya ranta a na kare.

“Mahaifiyar jaririyar mai shekara 16 ta je ofishin ’yan sanda, inda aka ba ta takardar da za ta ba ta damar zuwa asibiti domin a duba lafiyar ’yar tata.

“Sai dai wajen misalin karfe 11:00 na daren Talata, jami’anmu da ke ofishin Ijora Badiya sun cafko shi a inda yake buya.”

Benjamin ya kuma ce da wacce take karar da wanda ake zargin sun bayar da bayansu, inda ta ce wanda ake zargin ya amsa laifin lokacin da ake yi masa tambayoyi.