✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashi yana lalata da ‘mahaukaciya’ a Suleja

Ba don jami’an tsaro ba, da watakila na yi lalata da ita.

An kama wani matashi mai suna Haruna Musa yana lalata da wata mata mai tabin hankali a Unguwar Gwari Kwamba da ke Karamar Hukumar Suleja ta Jihar Neja.

Kafin ’yan sanda su yi awon gaba da wanda ake zargin, wani hoton bidiyo da wani ganau mai suna John Daniel ya nuna wa wakilinmu, ya nuna cewa ba a kai ga matakin turmi da tabarya ba a kokarin yi wa matar fyade.

Sai dai bidiyon ya nuna yadda matashin mai kimanin shekaru 21 ke kokarin zakke wa matar tana tsala ihu, lamarin da ya ankarar da jama’a har aka kai mata dauki.

Matashin wanda aka samu da kullin wasu abubuwa da ake kyautata zaton tabar wiwi ce, ya dora alhakin laifinsa a kan shaye-shaye da kuma la’antar da mutanen kauyensu ke yi masa.

Haka kuma, ya ce tsiraicin matar da ya bayyana ne ya sanya sha’awarsa ta motsa har ya yi kokarin aikata fasadi da ita.

Ya ce, “Ba don jami’an tsaro ba, da watakila na yi lalata da ita. Ban san me yake damu na ba a yanzu.

“Don Allah a yafe don ban wuce shekara 21 a duniya ba.

“Ina da abubuwa da yawa a raina. Matsalolin da suke damuna sun fi karfina kuma ba ni da wanda zai taimaka min.”

Bayanai sun ce doka ta yi tanadin daurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifi makamancin wannan, kasancewar matar tana da tabin hankali wanda hakan bai ba ta damar bayar da izinin a kusance ta ba.