✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matashi mai kai wa Boko Haram kwayoyi

Dan kasar Chadi mai yi wa Boko Haram safarar miyagun kwayoyi daga Najeriya ya shiga hannu

Dubun wani matashi dan kasar Chadi da ke yi wa kungiyar Boko Haram safarar miyagun kwayoyi daga Najeriya ta cika.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sun damke dillalin kwayoyin ne da kilogram 21.7 na Tramol da kuma kilogram 15.7 na Exol, yana shirin barin Jihar Taraba zuwa kasar Chadi, inji kakakin Hukumar, Femi Babafemi.

Ya ambato Kwamandan NDLEA a Jihar Taraba, Suleiman Jadi na cewa matashin ba ya jin wani yare sai Faransanci da Larabci, “Da muka bincike shi sai suka gano cewa yana daga cikin manyan dillalan kwayoyin da ke kai wa mayakan Boko Haram.

“A wurin binciken ne aka gano kwayoyin da ya siyo daga Onitsha, Jihar Anambra, a boye a cikin sabbin jakunkunan hannu na mata da takalma,” inji Babafemi.

Kama dan kasar Chadin da aka yi ranar Laraba na zuwa ne bayan a makon jiya an cafke wani dan kasar Jamhuriyar Nijar mai shekara 70 da ke yi wa Boko Haram fasakwaurin miyagun kwayoyi.