✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashi kan zargin satar wayar lantarki a Kano

Matashin ya shiga hannu bayan da dubunsa ta cika.

Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC), sun cafke wani matashi mai shekara 23 bisa zargin satar wata wayar lantarki a Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

An tabbatar da kamen ne a wata sanarwa da kakakin hukumar na jihar, DSC Ibrahim Idris-Abdullahi, ya fitar ranar Alhamis a birnin na Dabo.

Ya ce wanda ake zargin ya shiga wani gini ne da ke kan titin Bompai da ke yankin Karamar Hukumar Nassarawa, inda aka kama shi yana yanko wayar wutar mai tsayin mita 21.

“Wanda ake zargin, wanda ke zaune a unguwar Yakasai a Kano, an kama shi ne a yayin da jami’an tsaron da ke cikin harabar gini ke aiki suka hange shi,” inji shi.

Idris-Abdullahi ya ce an kammala bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.